Home Labaru Sakon Maulidi: Tijjani Ramalan Ya Roki Musulmi Su Yi Koyi Da Halayen...

Sakon Maulidi: Tijjani Ramalan Ya Roki Musulmi Su Yi Koyi Da Halayen Manzon ALLAH S.A.W

213
0

Shugaban kamfanin sadarwa na ATAAR da ya mallaki Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi koyi da halayen Manzon Allah, a daidai lokacin da ake cigaba da gudanar da bikin Maulidi.

Tijjani Ramalan ya bayyana hakan ne a cikin sakon murnar
bikin Maulidi da ya fitar, inda ya bukaci jama’ar musulmi su
rungumi halayen Manzon Allah na so da taimakon juna da nuna
jin kai a tsakanin al’umma.

Alhaji Tijjani Ramalan ya ƙara da cewar hakika haihuwar
Manzon Allah ya kasance alheri da nasara wadda ta game
dukkanin mutane sakamakon yadda haihuwar ta kawo haske da
rahama a duniya gaba ɗaya.

Shugaban na kamfanin ATAAR ya shawarci dukkanin jama’a su
yi amfani da wannan lokaci na bikin Maulidi wajen sanya
Najeriya cikin addu’ar Allah ya fitar da ita daga manyan
matsalolin da ta tsinci kanta a cikin na tsaro da tsadar rayuwa.

Leave a Reply