Home Labaru Sai Mun Sauka ‘Yan Nijeriya Za Su Riƙa Yaba Ayyukan Alherin Mu...

Sai Mun Sauka ‘Yan Nijeriya Za Su Riƙa Yaba Ayyukan Alherin Mu – Sanata Lawan

172
0

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce mafi yawan ‘yan Nijeriya su na kwana da tashi a cikin farin ciki game da ‘yan majalisa.

Sanata Lawan, ya ce sai ma bayan sun kammala wa’adin mulkin su ne akasarin ‘yan Nijeriya za su riƙa santin rubutawa da kuma furta kalaman alheri a kan Majalisar Dattawa da ta wakilai dangane da tarin nasarorin da su ka samar.

Ahmed Lawan ya bayyana haka ne, a wajen wani taron bikin taya shi murnar cika shekaru 63 a duniya da aka shirya a Abuja.

Kalaman Sanatan dai su na  zuwa ne, a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke kushe ‘yan majalisa, bisa zargin cewa ba su tsinana komai wajen taka wa ɓangaren shugaban ƙasa da ministoci da sauran ma’aikatu birki.

Mafi ya wan ‘yan Nijeriya dai su na jin haushin majalisar tarayya da ta dokoki, cewa duk abin da shugaban ƙasa ya kai masu sai su sanya hannun amincewa ido-rufe.