Home Labaru Gwamna Yahaya Bello Ya Fatattaki Masu Karbar Haraji Daga Titunan Kogi

Gwamna Yahaya Bello Ya Fatattaki Masu Karbar Haraji Daga Titunan Kogi

56
0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya dakile duk ayyukan karbar haraji ba bisa ka’ida ba, sanna ya bada umarnin cewa duk shingayen da aka sa a babban titin Okene zuwa Lokoja a cire su.

Hakuma, gwamnan ya bada umarnin cire dukkan wuraren da aka tsare tare da rufewa a kan titunan jihar saboda karbar harajin da ba bisa ka’ida ba.

Yahaya Bello ya sanar da cewa, al’amurran su su na da matukar ban takaici ga masu ababen hawa da masu amfani da titunan jihar.

Wata majiya ta ce, Gwamnan ya makale ne a wani dogon layin ababen hawa da ke babban titin Okene zuwa Lokoja, sakamakon sakacin masu karbar harajin, lamarin da ya yi matukar kunyata shi, lamarin da ya sa ya sauka daga motar sa, sannan ya umarci jami’in tsaro mai kula da lafiyar sa ya tabbatar da an cire shingen nan take.