Home Labaru Sabon Shugaban Kamfanin Jiragen Saman Nijeriya Ya Yi Tonon Silili

Sabon Shugaban Kamfanin Jiragen Saman Nijeriya Ya Yi Tonon Silili

297
0

Tsawon lokacin da ‘yan Nijeriya su ke dakon jiran fara aikin
kamfanin jiragen saman Nijeriya da tsohon shugaban kasa,
Muhammadu Buhari ya alkawaranta, amma lamarin ya zama
bambara-kwai yayin da sabon shugaban kamfanin ya yi tonon
silili a wannan makon.

Shugaban kafanin jiragen saman Nijeriya Kyaftin Dayo Olumide, ya shaida wa kwamitin mai kula da harkokin sufurin jiragen sama na majalisar dattawa cewa, jirgin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar kwanakin baya cewa mallakar Nijeriya ba haka zancen ya ke ba.

Ya ce hayar jirgin aka dauko daga kasar Habasha kwanaki kadan aka sauya ma shi launi tare da rubuta sunan ‘Nigeria Air’ domin a yaudari ‘yan Nijeriya da masu ruwa da tsaki.

Kyaftin Dayo Olumide, ya ce idan Nijeriya za ta tafiyar da ragamar jirgi, dole ne kayan aikin sa su kasance masu rajista da Nijeriya, kuma sai an samu lasisi da izinin gudanarwa da sauran abubuwan da ke akwai, ya na mai tabbatar wa duniya da cewa jirgin da aka ce mallakin Nijeriya ne aron sa aka dauko na ‘yan kwanaki kuma tunin an maida wa masu shi kayan su.

Leave a Reply