Home Labarai Rushewar Gini: Mutum 3 Sun Kuɓuta A Abuja

Rushewar Gini: Mutum 3 Sun Kuɓuta A Abuja

298
0
Federal character news celebrity sports nigeria 2023 04 08T100646.480
Federal character news celebrity sports nigeria 2023 04 08T100646.480

Rundunar ƴansanda, ta tabbatar da rushewar wani gini da rahotanni suka ce mai hawa huɗu ne a yankin Garki.

Sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar ta ce ginin ya rushe ne a jiya Litinin da daddare.

Ta ce bayan samun kiran waya kan lamarin, kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igweh ya tura jami’an sa zuwa wurin.

an kuɓutar da mutum uku daga cikin ginin da ya rushe inda kuma aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta ankarar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa domin ta ɗauki ragamar zaƙulo mutanen da ƙasa ta danne.

Leave a Reply