Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Olukayode Adeolu
Egbetokun, ya yi Allah wadai da wasu jami’an ‘yan sanda da
su ka tuƙa mota su ka bi kan wani mutum a jihar Edo.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce shugaban ‘yan sandan ya ba jami’an ‘yan sandan da yanzu haka ke tsare a jihar Edo umarnin su hallara a helkwatar hukumar da ke Abuja ranar Litinin domin ɗaukar mataki a kan su.
A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga yadda jami’an ‘yan sandan su ka tuka wata mota tare da bin ta kan wani mutum da ake tunanin direban motar ne, lamarin da ya jefa mutanen da ke wurin cikin firgici.
Sanarwar, ta yi kira ga al’umma musamman mutanen garin Ekpoma su kwantar da hankulan su, tare da alƙawarta cewa rundunar ‘yan sandan ba za ta lamunci irin wannan mummunar aika-aika da wasu ɓata-garin jami’an ta ke yi ba.