Home Labaru Bam Ya Tashi Da Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara, Dogo Gudali, Ya Mutu

Bam Ya Tashi Da Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara, Dogo Gudali, Ya Mutu

212
0

Rahotanni na cewa, kasurgumin shugaban ‘yan bindiga da ya
addabi al’ummar jihar Zamfara Dogo Gudali ya mutu.

Wata majiya ta ce, Gudali ya hadu da ajalin sa ne sakamakon tashin Bom da wasu ‘yan kungiyar sa na ta’addanci su ka dasa.

Majiyar ta ce, ‘yan ta’addan sun dasa Bom din ne domin kawar da dakarun rundunar soji ta Operation Hadarin Daji, wadanda ke aikin fatattakar su a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum.

Rahotanni sun ce an dasa Bom din ne domin sojoji, amma sai ya tashi kafin lokaci ya kashe shugaban yan bindigar Dogo Gudali da wasu mayakan sa.

Dogo Gudali da tawagar sa dai sun dade su na addabar yankunan Anka da Gummi da Bukkuyum da wasu yankuna na jihohin Sokoto da Kebbi.

Leave a Reply