Home Labaru Rundunar Sojin Nijeriya Ta Ƙaddamar Sabbin Tankokin Yaƙi 60 Daga China

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Ƙaddamar Sabbin Tankokin Yaƙi 60 Daga China

11
0

Rundunar sojin Nijeriya, ta ƙaddamar da wasu sabbin tankokin yaƙi guda 60 daga kasar China domin yaƙi da matsalolin tsaro da ake fuskanta.

Yayin da ya ke ƙaddamar da sabbin tankokin a barikin soji na Jaji da ke Kaduna, babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ce rundunar sojin ta ɗaukimatakin ne domin tabbatar da tsaron Nijeriya da al’ummar ta.

Ya ce sabbin tankokin yaƙin dai za su ƙarfafa ƙoƙarin da rundunar ke yi na yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas, sannan za su taimaka wajen kawar da masu tada ƙayar baya tare da samar da zaman lafiya a Nijeriya.