Home Labarai Rundunar Sojin Najeriya Ta Kaddamar Da Bincike

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kaddamar Da Bincike

279
0

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike kan kisan da aka yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.


Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar ta biyu ta Operation Hadin Kai, Kennedy Anyawu, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Damaturu.


Rundunar ta ce tuni ta kama sojoji biyu, kofur John Gabriel da kofur Adamu Gideon a kan batun kisan malamin.


Rundunar sojin ta ce da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ne za su gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.


Kazalika rundunar ta kuma kafa wani kwamiti da zai bankado yadda lamarin ya auku, inda tace da zaran an kammala bincike aka gano wadanda suka aikata kisan to lallai za su fuskanci hukunci da ya kamata.


A ranar Juma’ar da ta wuce ne aka kashe malamin addinin Musuluncin na jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami, a lokacin da yake tuƙa motar sa a kan hanyar zuwa Gashua daga Nguru.

Leave a Reply