Home Labarai Najeriya Na Taimaka Wa Al’ummar Ta Da Suka Makale A Hadaddiyar Daular Larabawa

Najeriya Na Taimaka Wa Al’ummar Ta Da Suka Makale A Hadaddiyar Daular Larabawa

123
0

Gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki tare da mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa wajen taimaka wa al’ummar ta da suka makale a Dubai.


Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Francisca Omayuli, cikin wata sanarwa ta ce ofishin jakadancin Najeriyar da ke Dubai na aiki tukuru wajen tattara bayanan wadanda suka makale a can domin samar musu da takardun da suka dace wajen dawo da su gida.


Ta kuma musanta zargin da ke cewa ofishin jakadancin ya yi watsi da ‘yan Najeriya da suka makale a Dubai, tana mai cewa a yanzu ofishin na aiki wajen taimaka wa ‘yan Najeriya 300 da ke tsare a ofishin hukumar kula da shige da fice ta Dubai.


Francisca Omayuli, ta ce sai an bi hanyoyin da dokar kasar ta tanada kafin a samar wa wadannan mutum 300 takardun da suka dace na dawo da su gida, domin kuwa an tsare su a can ne bisa dalilai da dama da suka hada da dadewa a kasar, da batar fasgon su da rashin takardun da suka dace musamman ga yara kanana.


A kwanan baya ne dai wani bidiyo ya rinka yawo a kafafan sada zumunta inda aka nuna wata mata da tace ita ‘yar Najeriya ce tana kira ga gwamnati ta taimaka musu tare da zargin ofoshin jakadancin Najeriya da ke Dubai da nuna halin ko-in-kula a kan su.

Leave a Reply