Home Labaru Rufe Iyakoki: Kasar Nijar Ta Haramta Shigo Da Shinkafa Zuwa Nijeriya

Rufe Iyakoki: Kasar Nijar Ta Haramta Shigo Da Shinkafa Zuwa Nijeriya

565
0

A bisa tafarki bin kundin tsarin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS, kasar Nijar ta haramta shigo da shinkafa zuwa Nijeriya, biyo bayan hukuncin da gwamnatin Nijeriya ta zartar na rufe iyakokin ta na kan tudu.

Idan dai za a iya tunawa, tun a ranar 20 ga watan Agusta na shekara ta 2019, gwamnatin Nijeriya ta rufe iyakokin ta na kan tudu da ke yankunan da su ka hada da Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa ta Yamma.

Rahotanni sun ce, gwamnatin kasar Nijar ta dauki matakin haramta shigo da shinkafar ne, biyo bayan hukuncin da gwamnatin Nijeriya ta yanke na rufe iyakokin ta, bisa manufar haramta shigo da kayayyakin fasa-kwauri domin bunkasa tattalin arziki.

Sanarwar dai, ta fito ne daga bakin shugaban hukumar hana fasa-kwauri ta kasa Kanar Hameed Ali, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja, inda ya ce bayan nan ne kasar Nijar ta haramta shigo da shinkafa Nijeriya, sakamakon rufe iyakokin kan tudu na kasar nan.