Home Labaru Kasafin 2020: Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Zaman Ta Tsawon Makonni Biyu

Kasafin 2020: Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Zaman Ta Tsawon Makonni Biyu

208
0

Majalisar dattawa ta dakatar da zaman ta na tsawon makonni biyu, domin ta ba ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya damar kare kasafin kudin da su ke sa ran kashewa a shekara mai zuwa.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ne ya sanar da dage zaman majalisar a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce majalisar ta zartar da hukuncin dakatar da zaman ta domin samun damar tuntubar ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya a kan kare kasafin kudaden sun a shekara ta 2020.

Tun bayan gabatar da kasafin a ranar 8 ga watan Oktoba, Sanata Ahmed Lawan ya ba kowace ma’aikata ko hukumar gwamnati umurnin ta je gaban majalisar domin kare kasafin kudin ta. Shugaban majalisar ya cigaba da cewa, za a dauki tsawon makonni biyu gabanin dukkan ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnati su kare kasafin kudin su.