Home Labaru Rikicin Zaria: ‘Yan Shi’a Sun Gabatar Da Shaidar Cewa El-Zakzaky Ya Makance

Rikicin Zaria: ‘Yan Shi’a Sun Gabatar Da Shaidar Cewa El-Zakzaky Ya Makance

1397
0

Mabiya akidar shi’a sun gabatar wa kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya wasu shaidu da ke nuna cewa idon shugaban su Ibrahim El-Zakzaky na hagu ya makance.

‘Yan shi’ar sun ce, yayin harin da sojoji su kai wa malamin a gidan sa da ke Zaria ne su ka harbe shi a idon sa na hagu, inda su ka gabatar da wani hoto da ke nuna shaidar cewa El-Zakzaky ya samu matsala a idon shi.

Sakataren kungiyar Abdullahi Mohammed Musa, ya ce ziyarar da kungiyar likitoci da wasu daga cikin ‘yan kungiyar kare hakkin dan Adam su ka kai wa malamin ta tona asirin irin cin zarafin da ake yi wa malamin.Ya ce jami’an tsaro sun harbe shi a idon sa na hagu, inda idon ya fito a lokacin da su ka kai hari gidan sa da ke Zaria a shekara ta 2015.

Leave a Reply