Home Labaru Wata Sabuwa: Malamai Sun Ja Hankalin El-Rufa’i A Kan Kudirin Dokar Binne...

Wata Sabuwa: Malamai Sun Ja Hankalin El-Rufa’i A Kan Kudirin Dokar Binne Gawa

462
0
Babu Gudu Babu Ja Da Bayaa Dokar Hana Fita Ranar Sallah- Gwamnati Kaduna
Babu Gudu Babu Ja Da Bayaa Dokar Hana Fita Ranar Sallah- Gwamnati Kaduna

Majalisar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna, ta bukaci Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da kudirin dokar binne gawa da Majalisar Dokoki ta Jihar ta mika masa domin neman amincewar sa.

A cikin wani jawabin bayan taro da da majalisar ta fitar dauke da sa hannun sakataren ta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu da shugbanta Shaykh Ibrahim Nakaka, ta ce kudirin ya saba wa koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W).

Daga cikin abubuwan da kudirin ya kunsa dai, akwai bukatar a yi rajistar jariran da aka haifa a ofishin karamar hukuma, kuma a sanar da hukuma idan an yi rasuwa ko an haifi jariri babu rai, sannan jami’an karamar hukumar za su bada wata takarda a cike kafin a bada izinin binne gawa. Majalisar malaman, ta kuma bukaci gwamnatin jihar Kaduna ta gaggauta kawo karshen rikice-rikicen da ake fama da su a Kajuru da wasu sassa na jihar.

Leave a Reply