Home Labaru Rikicin Sudan: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Gayyaci Ministan Ƙasashen Waje

Rikicin Sudan: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Gayyaci Ministan Ƙasashen Waje

427
0

Majalisar wakilai za ta gana da ministan harkokin wajen
Nijeriya Geoffrey Onyema, da jami’an ƙungiyar ‘yan Nijeriya
mazauna ƙetare da na hukumar bada agajin gaugawa ta ƙasa
domin sanin halin da ‘yan Nijeriya da su ka maƙale a rikicin
Sudan ke ciki.

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya bayyana haka a zauren majalisar, inda ya ce abin taƙaici ne rikicin Sudan ya rutsa da ‘yan Nijeriya da ke zama a ƙasar.

Ya ce an yi shiri domin tabbatar da an kwaso ‘yan Nijeriya da su ka haɗa da ɗalibai da ‘yan kasuwa da sauran masu sana’o’i cikin kwanciyar hankali ba tare da ɓata lokaci ba.

Femi Gbajabiamila, ya buƙaci shugaban kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar wakilai ya gayyaci ministan harkokin wajen Nijeriya, da jami’an ƙungiyar ‘yan Nijeriya mazauna ƙetare da na hukumar bada agajin gaugawa zuwa zauren majalisar domin su bada bahasi a kan halin da ake ciki
game da aikin kwaso ‘yan Nijeriya daga Sudan.

Gbajabiamila ya ce majalisar wakilai ta na sane da irin wahalhalun da ake fuskanta game da aikin kwaso ‘yan Nijeriya daga kasar Sudan.

LEAVE A REPLY