Home Labaru Rikicin Sudan: An Gudanar Da Zanga-Zangar Tilasta Wa Sojoji A Sudan Mika...

Rikicin Sudan: An Gudanar Da Zanga-Zangar Tilasta Wa Sojoji A Sudan Mika Mulki Ga Farar Hula

283
0

Dubun mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan, sakamakon kiran da ‘yan adawa suka yi na tilasta wa sojoji gaggauta mika mulki ga hannun fararar hula.

Kawancen samar da ‘yanci da kuma sauyi a Sudan, wanda suka kunshi kungiyoyi da jam’iyyun adawa da mulkin hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir, sun bukaci a gudanar da gangami da ake hasashen cewa, zai tara mutane fiye da miliyan daya a dai-dai lokacin da sojojin ke cewa, a shirye suke su saurari bukatun al’umma.

Mutane da dama, wasu a cikin motoci wasu kuwa a cikin jirgin kasa daga sassa daban daban na kasar ne suka halarci zanga-zangar, wadda aka shirya kwana guda bayan wasu kusoshin kasar uku sun yi marabus daga mukaman su, sakamakon cijewar tattaunawar da aka fara a kan batun kafa sabuwar gwamnatin riko.

Mahalarta gangamin, sun rika rera taken cewa, mulkin farar hula muke bukata, yayin da wasu ke cewa, mun fito ne domin kare nasarar juyin juya halin da ya yi awon gaba da mulkin al-Bashir.

Alkalai da dama a cikin bakaken tufafin su ne suka yi tattaki daga ginin kotun kare tsarin mulkin kasar zuwa inda ake gudanar da gangamin, kuma a cewar su sun fito ne domin tabbatar da ‘yancin bangaren shari’a da kuma hana ‘yan siyasa yi masu shishigi.

Leave a Reply