Biyo bayan gudunmuwar dala 500,000, kwatankwacin kusan naira miliyan 180 da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba kasar Guinea Bissau, lamarin ya haifar da cece-kuce musamman a shafukan sada zumunta na zamani.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya ce wannan gudummawa ce da kasar Guinea Bissau za ta yi amfani da ita domin gudanar da zabe a kasar.
Sauran kayayyakin da Nijeriyar za ta tallafa wa kasar da su kuma sun hada da akwatunan jefa kuri’a 350, da baburan hawa guda 10, da kuma motocin a-kori-kura guda biyu.
Shugaba
Buhari ya umarci ministan harkokin kasashen wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya
wakilce shi a kasar ta Guinea.
You must log in to post a comment.