Home Labaru Rikicin Shi’a: Dole A Hukunta Wadanda Aka Samu Da Laifi – Buhari

Rikicin Shi’a: Dole A Hukunta Wadanda Aka Samu Da Laifi – Buhari

680
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gargadi ‘yan Shi’a su dakatar da zanga-zanga da kuma tashin-tashinar da su ke aiwatarwa ko su fuskanci fushin hukuma.

Buhari ya ce jama’a mazauna birnin Abuja da sauran wurare a fadin Nijeriya su fita zuwa harkokin su kamar yadda su ka saba ba tare da wani dar-dar ba.

Karanta Labaru Masu Alaka: Kasar Iran Ta Nemi A Aike Mata Da Zakzaky

Idan dai ba a manta ba, wanin dan bautar kasa Precious Owolabi da ma’aikacin gidan talbijin na Channels TV da mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan Abuja Usman Umar, su na daga cikin wadanda su ka rasa rayukan su a Abuja sakamakon zanga-zangar ‘yan shi’an da ta rikide zuwa fada. Shugaba Buhari, ya ce wadanda su ka aikata mummunan ta’adin ya zama wajibi a hukunta su, saboda gwamnati ba za ta zuba ido ta na kallo ana yi wa dokokin kasa karan-tsaye ba.