Home Labaru Rikicin Shi’a: An Ji Ta Bakin Shaidu A Shari’ar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Rikicin Shi’a: An Ji Ta Bakin Shaidu A Shari’ar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

409
0
Ibraheem El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Shi’a Ta Nijeriya
Ibraheem El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Shi’a Ta Nijeriya

A karon farko, shaidu sun bada bahasi a shari’ar da ake yi wa shugaban ƙungiyar ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa Malama Zenatudden a Babbar Kotun Jihar Kaduna.

Laifuffukan da ake zargin su da aikatawa sun haɗa da tada zaune tsaye da tunzura jama’a lokacin da mabiyan sa su ka samu sabani da da sojoji a birnin Zariya a shekara ta 2015 a yayin bukin maulidi

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun bayyana cewa, sama da mabiyan sa 300 ne sojoji suka yi musu kisan gilla sannan aka ji ma Sheikh El-Zakzaky mummunan raunuka

Tun lokacin ne ake tsare da shi da matar sa, amma wata kotu kwanakin baya ta wanke wasu mabiyan sa sama da 100 daga aikata laifi da aikata laifun da ake tuhumar El-zakzaky

A shekara ta 2016 ne babbar kotun tarayya dake Abuja ta bada umarnin sakin el-zakzaky tare da mai dakinsa amma hukumomi suka ki bin umarni na kotun

Leave a Reply