Home Labaru Cin Hanci: Magu Ya Ki Halartar Gayyatar Da Hukumar CCB Ta Yi...

Cin Hanci: Magu Ya Ki Halartar Gayyatar Da Hukumar CCB Ta Yi Ma Shi

194
0

Dakataccen Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu, ya ki amsa gayyatar da Hukumar Ladaftar da Ma’aikata ta Kasa CCB ta yi ma shi.

Hukumar CCB dai ta aika wa Magu wasikar neman ya bayyana gaban ta a helkwatar ta da ke Abuja, bayan ta zarge shi da karya ka’idar aikin gwamnatin tarayya.

Hukumar ta nemi Magu ya kai mata takardun shaidar adadin kadarorin da EFCC ta karba a hannun wadanda su ka wawuri kudin gwamnati, sannan ya je da dukkan takardun gidaje ko kadarorin baki daya.

Babban Lauyan Magu Wahab Shittu, ya ce bai sani ba ko Magu zai amsa gayyatar ko ba zai amsa ba, domin bai sanar da shi wasikar gayyatar da aka yi ma shi ba.