Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, sun sasanta rikicin da ke tsakanin su, tare da kudurin yin aiki tare domin samun nasarar jam’iyyar a babban zaben badi.
A wani taron sirri ne Atiku Abubakar ya yi wata ganawa da Gwamna Bala Mohammed da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a nan Abuja a daren ranar Talata.
Da yake bayyana sakamakon taron a safiyar ranar Larabar nan a shafin sa na Facebook, Atiku ya rubuta cewa a daren laraba ya karbi bakuncin wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP a nan Abuja, sun tattauna halin da jam’iyyar da al’ummar kasa ke ciki.