Home Labaru Rashin Sulhu: PDP Na Shirin Gudanar Da Taron Zaben Fidda Gwani

Rashin Sulhu: PDP Na Shirin Gudanar Da Taron Zaben Fidda Gwani

108
0

Jam’iyar PDP, ta ce yanzu haka ta na da ‘yan takarar shugaban kasa 17 daga yankin arewa da kudancin Nijeriya, wadanda ta ke sa-ran shiga zaben fidda gwani da su.

Mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar arewa Ambasada Umar Iliya Damagum ya bayyana haka, yayin da ya ke amsa tambaya a kan zaman sasantawa tsakanin ‘yan takara 4 na arewa da Janar Babangida ya jagoranta.

A wajen taron sulhun da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Sanata Bukola Saraki su ka yi nasara, bai samu sa hannun gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ba, yayin da tun farko Atiku Abubakar bai shiga sulhun ba

Ambasada Damagum, ya ce ‘yan takarar su na da hurumin bin dabarun su na hulda da juna, amma ba a karkashin jam’iyya ko tsarin ta aka gudanar da taron mutanen hudun ba.

Gwamna Bala Muhammad, ya ce ko ma me za a ce ba ya da wata rashin jituwa da sauran ‘yan takara, musamman ma gwamna Tambuwal.