Home Home Rikicin Aure: Matashiya Ta Kai Mahaifinta Ƙara Kotu A Kaduna

Rikicin Aure: Matashiya Ta Kai Mahaifinta Ƙara Kotu A Kaduna

157
0

Wata matashiya Halima Yunusa ta kai mahaifinta ƙara kotun shari’ar musulunci a Kaduna kan zargin ƙin aurar mata masoyinta mai suna Bashir Yusuf.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa Halima ta shaida wa kotun cewa tana matuƙar son Yusuf amma iyayenta sun ƙi yarda su aura mata shi .

Mahaifin mai suna Ibrahim ya shaida wa kotun cewa yana sane da irin soyayyar da ke tsakanin ƴarsa da Yusuf, amma a cewarsa, Yusuf bai kammala cika duka sharuɗan aure ba.

Mahaifin ya yi ikirarin cewa ya faɗa wa saurayin ƴarsa da ya turo iyayensa amma kusan shekara guda bai dawo ba.

Sai bayan shekara guda ya zo ya ɗauki ƴar suka tafi kwana uku ba su dawo ba inda daga baya suka samu labarin cewa sun dawo sun tafi gidan ƴar uwar mahaifin, kamar yadda ya shaida wa kotun.

Ya ce bayan haka ne suka kai su ƙara wurin ƴan sanda inda aka kama su kuma aka hukunta su inda bayan sakinsu daga wurin ƴan sanda kuma sai suka gudu zuwa Abuja.

Mahaifin yarinyar ya ce daga baya ya haɗu da mahaifin Yusuf inda har mahaifin Yusuf ɗin ya gargaɗe shi kan cewa ba zai yarda ɗansa ya auri ƴarsa ba.

Daga baya alƙalin kotun bayan jin duka ɓangarorin ya bayar da umarnin cewa mahaifin yaron wato Yusuf ya bari ɗansa ya auri Halima idan kuma bai bari ba kotu za ta ɗaura musu aure.