Home Labaru Rikicin APC A Kano: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri Da Shekarau

Rikicin APC A Kano: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri Da Shekarau

65
0
Jigo a Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya yi ganawar sirri da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Jigo a Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya yi ganawar sirri da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Tinubu da Sanata Shekarau sun sa labule ne kwana kadan bayan rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Kano ya dauki sabon salo.

Gabanin ganawar sa da Malam Ibrahim Shekarau, Tinubu ya yi irin wannan ganawa da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a kwanakin baya.

Bangaren Ganduje da na Sanata Shekaru dai na zaman doya da manja, har ta kai ga kowannen su ya zabi shugabannin sa daban, a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar a matakin jiha.

A makon da ya gabata ne dai kotu ta tabbatar da Ahmadu Haruna Zago wanda bangaren Shekarau a matsayin halastaccen Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.