Home Home Zargin Zagon Kasa: DSS Ta Kama Janar Idris Bello Dambazau A Kano

Zargin Zagon Kasa: DSS Ta Kama Janar Idris Bello Dambazau A Kano

32
0
Rahotanni na cewa, Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama Janar Idris Bello Dambazau (Rtd), Manajan Darakta na Hukumar Kare masu sayen Kayayyakin ta jihar Kano bisa zargin zagon kasa ga tattalin arzikin kasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama Dambazau ne bisa zargin sa da rufe wasu gidajen mai guda bakwai a babban birnin jihar, lamarin da rundunar ‘yan sandan sirrin ta ce bai dace ba.

Wani babban jami’i a hukumar ta DSS a jihar Kano ya ce an kama Dambazau ne a wannan Lahadin bayan da aka yi yunkurin bude gidajen man.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada Janar Dambazau (Rtd) cikin watan Satunbar wannan shekara ta 2021 a matsayin shugaban Hukumar.