Home Labarai Rikicin APC: Ɓangaren Shekarau Ya Ce Zai Ɗaukaka Ƙara

Rikicin APC: Ɓangaren Shekarau Ya Ce Zai Ɗaukaka Ƙara

154
0

Ɓangaren jam’iyyar APC da ke rikici da na Ganduje a jihar
Kano, ya ce zai ɗaukaka ƙara a kan hukuncin kotu da ya ce
shugabancin ɓangaren gwamnan ne halastacce.

Shugaban bangaren Ahmadu Haruna Zago ya shaida wa
manema labarai cewa, za su yi biyayya ga hukuncin amma za su
ɗaukaka ƙara, kuma Lauyoyin su sun fara nazari a kan hukuncin
kotun.

A zaman Kotun Ɗaukaka Ƙara dai ta ce Babbar Kotun Abuja ba
ta da hurumin yin hukunci a kan rikicin, sannan ta ce
shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce ba na Haruna Zago
ba.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne bangaren
Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam’iyyar APC
ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Ganduje a matsayin shugaban
kwamatin sasanta rikicin.