Home Labaru Rikice-Rikice: Gwamnati Ta Yi Watsi Da Rahoton Kungiyar Tarayyar Turai

Rikice-Rikice: Gwamnati Ta Yi Watsi Da Rahoton Kungiyar Tarayyar Turai

263
0
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai

Danga ne da batun rikice-rikicen da ke faruwa a Nijeria da kuma katsalandan da Tarayya Turai ta yi kan wannan lamari wanda har ta fitar da wani rahoto da ke nuna gazawar gwamnatin kan wannan matsala,

Mai bai wa shugaban kasa Muhammdu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta yi watsi da wannan rahoto domin kuwa ba gaskiya ba ne.

Saboda kowace kasa babban abin da  ta fi ba muhimmanci  shi ne samun zaman lafiya, da samun zaman lafiya ne za rayu sannan a ci gaba da gudanar harkokin yau da kullum, saboda haka babu wata kasa da za a ce ta zura ido ta bari rikici na faruwa a kasar.

Garba ya ce a wurare irin su Benue, Taraba, Cross Riber  ma fi yawanci fadace-fadacensu na kabilanci ne. Ya ce, wasu da yawa daga cikin al’ummar irin wadannan yankuna ta sa dole suka yi wo gudun hijira. Ya ce ko tantama babu rikice-rikce sun sha afkuwa tsakanin Fulani da manoma, amman bisa kokarin da wannan gwamnati ke yi an samu sauki matuka.