Home Labaru Ricikicin APC A Zamfara: ‘kwamitin buni ya yi wa kotu karan-tsaye’

Ricikicin APC A Zamfara: ‘kwamitin buni ya yi wa kotu karan-tsaye’

642
0

’Yan jam’iyyar APC bangaren Sanata Kabir Marafa a Zamfara sun ce matakin da kwamitin riko karkashin jagorancin Gwamnan jihar Yobe Mai mala Buni, ya dauka na korar shugabansu Alhaji Sirajo Garba ya sabawa umurnin kotu.

A ranar 25 ga watan Yuni, 2020, Shugabannin APC suka zartar cewar kada wani dan jam’iyyar ya shigar da kara kotu, wadanda kuma suka shigar da karar su janye domin bai wa kwamitin damar yin sulhu a cikin gida.

Sai dai kuma kakakin bangaren Marafa, Alhaji Bello Bakyasuwa ya shaidawa manema labarai cewa, Kotu ta rushe shugabannin jam’iyyar kuma ta ce a gudanar da sabon zabe.

Acewar Alhaji Bello bai kamata a dauki matakin kora wani Dan Jam’iya a dai-dai wannan lokaci da ake kokarin ganin anyi sulhu tareda farfado da Jam’iyar ba.

Inda yace matakin ba zai magance matsalar ba

LEAVE A REPLY