Home Labaru Kasuwanci Karin Farashin Man Fetur: ‘Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Korafi

Karin Farashin Man Fetur: ‘Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Korafi

283
0

Al’ummar kasar nan na ci gaba da nuna bacin ransu kan karin farashin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi daga N149 wanda shi ne na uku a cikin wata uku.

A cikin wata sanarwar da Hukumar Kula da Farashi Albarkatun Man Fetur (PPMC) ta fitar ta ce dillallan man za su rika sayen litar fetur a kan N151.56.

Hakan ta sa Kungiyar Dillalai Mai Masu Zaman Kansu (IPMAN) ta umurci masu gidajen man das u sayar da litar man fetur din a kan Naira 162.

Tuni rahotanni suka tabbatar da cewa tuni wasu gidajen mai sun kara farashin musamman a birnin Legas.

Yayin da ’yan Najeriya ke ci gaba da caccakar karin, wanda ya zo kwana bayan da kanfanonin wutar lantarki suka kara farashi.

Shugaban kungiyar IPMAN a Jihar Kano, Alhaji Bashir Danmalam, ya ce suna tattaunawa kan farashin da za su sayar da fetur nan gaba.

Masu ababen hawa da motocin haya da ma’aikata da masu sana’o’i da sauran ’yan Najeriya sun bayyana takaicin su akan karin kudin man.