Home Labaru Rayuwar Shonekan Ta Koya Wa ‘Yan Nijeriya Son Ci-Gaban Ƙasa – Buhari

Rayuwar Shonekan Ta Koya Wa ‘Yan Nijeriya Son Ci-Gaban Ƙasa – Buhari

108
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana alhinin rasuwar tsohon shugaban kasa na rikon kwarya Cif Ernest Shonekan.

Buhari ya bayyana rayuwar Shonekan a matsayin wadda ta koya wa ‘yan Nijeriya cewa ƙauna da kuma son ci-gaban Nijeriya sun wuce maganar riƙe wani muƙami da siyasa.

A cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar, shugaba Buhari ya ce a madadin gwamnatin Nijeriya, ya na miƙa ta’aziyyar sa ga matar Shonekan Margaret da ‘yan’uwan sa, da kuma gwamnatin Jihar Ogun.

Cif Shonekan dai ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Legas kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

RAHOTO: KANO

ZIRGA-ZIRGA: DIREBOBIN ADAIDAITA SAHU SUN SAKE TSUNDUMA YAJIN AIKI A JIHAR KANO

Al’ummar Birnin Kano sun shiga tsaka-mai-wuya, sakamakon sake shiga yajin aiki da direbobin adaidaita sahu su ka yi.

Wakilin mu Abdulhadi Ibrahim Badawa ya yi nazari a kan lamarin, ga kuma rahoton da ya aiko mana…