Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Tafka Mummunar Barna A Kaduna

‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Tafka Mummunar Barna A Kaduna

53
0

‘Yan bindiga sun kai hari a yankin Gbagyi Villa da ke kan hanyar zuwa matatar mai ta Kaduna, inda su ka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da matar sa da wasu mutane.

Ya zuwa yanzu dai ‘yan jarida su na jiran martanin hukuma daga hukumomin tsaro kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wani mazaunin unguwar ya ce, lokacin da ‘yan bindigar su ka shiga cikin jama’a sai mutane su ka ranta a na kare, amma mutumin da ya yi kama da ‘yan banga ya tsaya ya na kokarin yin waya da wani abu kamar wayar Oba-Oba.

‘Yan bindigar da sun harbe mutumin ya mutu nan take, yayin da ake zargin cewa baya ga matar marigayin sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna unguwar sama da 10 a wani samame da ya dauki sama da sa’a daya.