Sakataren Gudanarwar Kungiyar Tuntuba ta Arewa wato ACF Alhaji Mohammed Sani Soba, ya kwanta dama.
Alhaji Mohammed Sani Soba ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi a ranar Asabar, 4 ga Satumba, 2021.
Sakataren Yada Labaran ACF, Emmanuel Yawe, shine ya tabbatar da hakan inda ya kara da cewa Rasuwar ta kada mu matuka a ACF,marigayin dai ya shafe shafe shekaru yana aiki har zuwa lokacin rasuwarsa.”
Ya bayyana mamacin da cewa mutumin kirki ne da ya hidimta wa kungiyar ta ACF a matsayin Sakataren Gudanarwa.
Mamacin tsohon Babban Sakatare ne a Gwamnatin Jihar Kaduna, bayan ya yi ritaya ya kama aiki da ACF a matsayin kwantaragi.
Sanarwar rasuwar da ACF ta fitar ta ce, “An haifi Soba ne a 1949 sannan ya yi karatu a cikin gida da kasashen waje a fannoni da dama na mulki da ayyukan majalisar dokoki.
Ya taba zama Akawun Majalisar Dokokin Jihar Kaduna.”













































