
Kungiyar Taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a kasar Afghanistan wacce za ta kasance karkashin jagorancin Mohammad Hasan Akhund.
Abdul Ghani Baradar kuma shi ne zai kasance Mataimakin Shugaban Kasa, yayin da Sirajuddin Haqqani zai kasance sabon Ministan Cikin Gida, kamar yadda kakakin kungiyar, Zabihullah Mujahid ya sanar yayin wani taron manema labarai a Kabul
Shugaban kungiyar Haqqani wanda hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI take nema ruwa a jallo shi ne ministan harkokin cikin gida.
Taliban ta kwace ikon kasar fiye da mako uku da suka gabata, inda suka kori gwamnatin da aka zaba.













































