
Yayin da ake fuskantar matukar zafin yanayi da kuma ibadar azumin watan Ramadan, yanzu haka jama’a na ci-gaba da kokawa bisa rashin tsayayyar wutar lantarki a fadin Nijeriya, lamarin da ya jefa al’uma da dama cikin mawuyacin hali.
Duk da cewa ‘yan Nijeriya sun samu ingancin wutar lantarki a ‘yan kwanakin da su ka gabata, amma lamarin ya kara dagulewa a ‘yan kwanakin nan, ta yadda aka fara fuskantar matsalar a lokacin zafi.
Mazauna birnin tarayyar Abuja da jihohin Neja da Nasarawa sun yi matukar kokawa a kan katsewar hasken latarkin, musamman a ‘yan kawakin nan da aka yi hutun bukukuwan Easter.
Lamarin dai ya sa mutane neman bayani dangane da halin kuncin da su ka samu kan su a ciki daga kamfanonin da ke aikin rarraba wutar lantarkin.
You must log in to post a comment.