Home Labaru Rashin Tsaro: Ƴan Majalisa Na Son Buhari Ya Duba Buƙatar Dokar Ta-Baci

Rashin Tsaro: Ƴan Majalisa Na Son Buhari Ya Duba Buƙatar Dokar Ta-Baci

78
0

Wasu yan majalisar dokokin Najeriya na ganin akwai bukatar a duba kiraye-kirayen da wasu gwamnatocin jihohi ke yi kan ya kamata shugaba Buhari ya sanya dokar ta-baci a kan tsaro domin a dakile aika-aikaryan bindiga.


A makon da ya wuce ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da irin wannan shawarar.
Ita ma `yar majalisar wakilan Najeriya, Hon Khadija Waziri Bukar Ibrahim ta ce ya kamata a duba hanzarin jihohin, saboda mai daki shi ya san inda ke masa yoyo.