Home Labaru Rashin Lantarki: Al’Ummar Karamar Hukumar Lere Sun Koka Da Halin Da Suke...

Rashin Lantarki: Al’Ummar Karamar Hukumar Lere Sun Koka Da Halin Da Suke Ciki

55
0
Lack of Electricity

Al’ummar karamar Hukumar Lere dake jihar Kaduna sun koka dangane da matsalar rashin hasken wutan lantarki da Suka Dade Babu a yanki, Sannan ba a dauki matakin gyarawa Dan Maido da ita ba.

Tsohon Dan majalisar dokokin jihar Kaduna Hon. Muhammad Kabir Doka, ya bayyana haka lokacin da yake Karin Haske dangane da matsalar Rashin Wutan lantarki da a karamar Hukumar ke fama das hi.

Ya ce Sama da Shekara Biyu Kenan Al’ummar yankin ke Cikin damuwa musamman Masu sana’o’i daban daban dake amfani da ita, ya ce matsalar ta janyo koma bayan tattalin arziki a karamar Hukumar dama jihar Kaduna baki Daya.

Muhd Kabiru ya Kara da cewa Idan akayi dubi da yadda Hasken Wutan lantarki ke kawo cigaba da habbakar tattalin arziki kamata Yayi Gwamnatin jihar Kaduna da Hukumar Rana Hasken lantarki suyi abin da yakamata a dawo da Wutan lantarki a karamar Hukumar 

Hon. kabiru Doka ya Kara da cewa Sama da Shekara guda kenan yakin ke cikin duhu, dan haka ya Roki Gwamnati da Hukumar raba lantarkin su dubi Al’ummar karamar Hukumar Lere da Idon Rahma wajan dawo da Hasken lantarkin kamar yadda aka Saba.