Home Labaru Kimiyya Bunkasa Noma: Dan Majalisa Ya Ce Nasarorin Buhari Ba Za Suyi Tasiri...

Bunkasa Noma: Dan Majalisa Ya Ce Nasarorin Buhari Ba Za Suyi Tasiri Ba Muddin Babu Tsaro

64
0
African-Agriculture

Wani ‘Dan Majalisar wakilai Yusuf Adamu Gagdi, ya ce duk kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na bunkasa noma da yaki da cin hanci da rashawa da gina hanyoyin jiragen kasa ba za su yi tasiri ba muddin ya kasa samarwa ‘yan Najeriya da tsaron da suke bukata domin gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Yusuf Adamu Gagdi, dake wakiltar mazabar Kanam da Kanke da kuma Pankshin daga Jihar Filato a Majalisar wakilan ya bayyana haka ne a budadiyar wasikar da ya rubutawa shugaba Buhari, domin janyo hankalin sa akan zub da jini da kuma kashe kashen da ake samu a sassan kasa.

Dan Majalisar wanda ya fito jam’iyya guda da shugaban kasa yace kundin tsarin mulki ya basu dama a matsayin su na ‘yan majalisu wajen janyo hankalin shugaban kasa domin gudanar da ayyukan da suka dace da kuma nuna masa inda ya dace ya yi gyara idan bukatar haka ta taso.

Yusuf Gagdi ya bayyana matukar damuwar sa akan yadda ‘yan bindiga ke kashe mutane a garuruwan dake cikin Najeriya ba tare da daukar matakin kare lafiyar su ba, yayin da rikici tsakanin makiyaya da manoma ke kara zafafa, tare da satar dalibai da kona garuruwa, a daidai lokacin da jami’an tsaron da ake saran zasu kare lafiya da dukiyoyin jama’a suka gaza gudanar da ayyukan su kamar yadda suka dace.

Dan majalisar yace hakki ne a wuyar su a matsayin su na wakilai su gabatar da bukatun jama’a da kuma koken su akan halin da suka samu kan su, kuma wannan ne dalilin da ya sa ya rubutawa shugaban kasa budadiyar wasika domin jan halin sa da kuma makusantar sa akan halin da jama’a suke ciki da kuma bukatar yin gyara cikin lokaci.