Home Labaru Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Tsohon Mijinta

Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Tsohon Mijinta

1197
0

Wata matar aure mai suna Auta Dogo Singe, ta kashe mijin ta mai suna Abdullahi Shaho a karamar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi don kawai ta na son auren ta ya mutu domin ta koma gidan tsohon mijin ta.

Rahotanni sun ce matar ta hada baki ne da wasu mutane biyu, wadanda su ka hada da wani Sahabi Garba da Garba Hassan a kauyen Sabon Gari da ke yankin Illo.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi Garba Muhammad Danjuma, ya ce matar ta kashe mijin ta ne saboda ta na son komawa gidan tsohon mijin ta Idris Garba.

Garba ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sanda ta kama matar tare da mutanen biyu da su ka hada baki da ita domin aikata kisan.

Ya ce rundunar ‘yan sandan ta na neman wasu mutane hudu, wadanda su ka hada da Yahuza Ibrahim da Murtala Abdullahi da Malam Nasiru da Dansilami, bisa zargin su da yi wa wani mutum fashin kudi Naira 253,000 da babur na hawa da wasu sauran kayan sa masu daraja.