Mahukuntan haɗaɗɗiyar daular larabawa sun taso keyar ƴan Najeriya 400 sakamakon zama a’ ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya ba bisa ka’ida ba, matakin da ke zuwa makwanni bayan dawo da bayar da biza da ƙasar ta yi ga al’ummar Najeriyar.
Rahotanni sun ce manyan hukumomin ƙasar da suka haɗa da na agaji da mai kula da ƴan cirani da masu kula da shige da fice da kuma hukumar yaƙi da safarar mutane baya ga jami’an ofishin babban mai bayar da shawara kan sha’anin tsaro na Najeriyar ne suka tarbi mutanen a babbar tashar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Rahotanni sun ce mutanen 400 sun ƙunshi mata 90 da kuma maza 310 waɗanda bayanai suka ce wasun su izinin zaman su a ƙasar ta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa ya ƙare amma suka ƙi ficewa yayinda wasun su suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
Galibi ƴan Najeriyar kan yi amfani da damar shiga ƙasar da nufin karatu ko kuma cinikayya amma sai su juye zuwa ƙwadago ba tare da takardun izinin yin aiki ba.
Haka zalika akwai bayanan da ke alaƙanta ƴan Najeriyar da aikata ba dai dai ba a ƙasashen musamman na gabas ta tsakiya lamarin da a lokuta da dama kan kaiwa ga korosu gida.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ƙasashe ke tiso ƙeyar ƴan Najeriyar ba, domin kuwa ko a Juma’ar da ta gabata sai da Turkiya ta kwaso ƴan Najeriyar 103 tare da miƙasu ga hukumar NEMA.