Home Labarai Rashin Amincewa: Afrika Ta Kudu Za Ta Kama ‘Yan Kasar Da Ke...

Rashin Amincewa: Afrika Ta Kudu Za Ta Kama ‘Yan Kasar Da Ke Yaƙi A Isra’Ila

378
0

Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Naledi Pandor ta bayyana cewa, za a kame ‘yan kasar da ke yaki a zirin Gaza tare da Dakarun tsaron Isra’ila yayin da suka komo gida.

Ta ce ta riga ta fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan Afrika ta kudu da suke yaki a shirye ta ke muddin suka dawo gida za a kama su, kuma tana fadin haka ne yayin taron nuna goyon baya ga Falasdinawa a farkon makon nan.

Afrika ta kudun dai ta riga tayi gargadi a shekarar da ta gabata kan cewa ‘yan kasar za su iya fuskantar hukunci in suka yi fada tare da sojin Isra’ila.

Afrika ta kudu dai na kan gaba cikin kasashe masu sukar yakin da isra’ila ke yi a Gaza wanda ya samo asali sakamakon kisan mutane sama da 1,200 tare da yin garkuwa da wasu fiye da 200 a watan Oktoba.

Kasar ta shigar da kara a kotun duniya domin duba ko Isra’ila na aikata kisan kiyashi kan Falasdinawan a Gaza.

Leave a Reply