Home Labarai Gasar Zakarun Turai: Dortmund Da Atletico Sun Kai Matakin Kwata Final

Gasar Zakarun Turai: Dortmund Da Atletico Sun Kai Matakin Kwata Final

38
0
1. Fussball Bundesliga, 1. FC Union Berlin vs Borussia Dortmund. Berlin, 02.03.2024 Jubel zum 0:1 durch Karim Adeyemi Borussia Dortmund, 27, Niklas Süle Borussia Dortmund, 25 1. Fussball Bundesliga, 1. FC Union Berlin vs Borussia Dortmund, Stadion An der Alten Försterei, Berlin 02.03.2024 DFL REGULATIONS PROHIBIT ANY USE OF PHOTOGRAPHS AS IMAGE SEQUENCES AND/OR QUASI-VIDEO. *** 1 Soccer Bundesliga, 1 FC Union Berlin vs Borussia Dortmund Berlin, 02 03 2024 Cheers for 0 1 by Karim Adeyemi Borussia Dortmund, 27 , Niklas Süle Borussia Dortmund, 25 1 Soccer Bundesliga, 1 FC Union Berlin vs Borussia Dortmund, Stadion An der Alten Försterei, Berlin 02 03 2024 DFL REGULATIONS PROHIBIT ANY USE OF PHOTOGRAPHS AS IMAGE SEQUENCES AND OR QUASI VIDEO Copyright: xBEAUTIFULxSPORTS/LucianoxLimax

A daren jiya Laraba ne aka kammala wasannin zagaye na biyu na gasar zakarun Turai, inda a yanzu aka samu kungiyoyi 8 da suka kai matakin dab da na kusa da na karshe a gasar ta bana.

A wasannin da aka yi a daren Laraba, Borussia Dortmund ta samu nasara akan PSV da ci biyu da nema, kuma ta samu nasarar ce bayan kwallayen da Jadon Sancho da kuma Marco Reus suka jefa mata, lamarin da ya ba Dortmund damar kai wa mataki na gaba a gasar ganin ta jefawa jumullar kwallaye 3 a dukkanin wasanni biyu da suka yi, yayin da PSV ta jefa kwallo daya tilo.

A dayan wasan kuwa, Atletico Madrid ce ta yi waje da Inter Milan a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Atletico Madrid ce ta samu nasara a wasan bayan da aka tashi da ci biyu da daya, sai dai duk da nasarar da ta samu sai da aka buga bugun daga kai sai mai tsaron gida, domin dukkanin kungiyoyin na da kwallaye biyu a ragar juna a dukkanin wasanni biyu da suka yi.

Da wannan nasara, a yanzu kungiyoyi 8 da suka samu nasarar tsallaka wa zagayen dab da na kusa dana karshe a gasar zakarun Turai sun hada da Arsenal da Barcelona da Bayern Munich da Atletico Madrid da kuma Borussia Dortmund.

A gobe Juma’a ne kuma za a hada yadda wadannan kungiyoyi za su kara da juma a wannan zagaye.

Leave a Reply