Home Labarai Rashin Ɗa’a Ga Alkalin Wasa: Hukumar Fa Ta Fara Tuhumar Kompany

Rashin Ɗa’a Ga Alkalin Wasa: Hukumar Fa Ta Fara Tuhumar Kompany

132
0
Match referee Darren England

Hukumar FA ta tuhumi mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Burnley Vincent Kompany bayan kalaman sa biyo bayan bashi jan kati a wasan da suka yi canjaras da kwallo 2 da 2 tsakanin su da Chelsea ranar Asabar da ta gabata.

Tun farko Kompany ya kalubalanci alkalin wasa Darren England game da bugun fenaritin da ya ba Chelsea dama jan katin da ya ba mai tsaron baya Lorenz Assignon, wanda manajan ya bayyana da abin da bai kamata ba.

Bayan tashi daga wasan Kompany wanda tsohon dan wasan Belgium ne da ya taka leda da Manchester City ya koka da cewa lamarin alkalin wasanni na ci gaba da tabarbarewa a Ingila batun da ya fusata hukumar FA.

Sanarwar da FA ta fitar ta tuhumi Kompany da rashin ɗa’a yayinda ta bashi daga yanzu zuwa ranar juma’a don yi mata bayani.

Sanarwar ta ce kalmomin da Kompany ya yi amfani da su a lokacin ana minti na 40 da faro wasan ya sabawa dokokin da ladubban hukumar ta FA.

Cikin wannan kaka kaɗai dai ƴan wasan Burnley 6 aka kora daga fili a wasanni 30 wanda ya zama mafi yawa da wata kungiya ta taba gani a Firimiyar Ingila.

Yanzu haka dai Burnley na matsayi na 19 ne a teburin na Firimiya yayinda ta ke shirin haduwa da Everton a ranar Asabar.

Leave a Reply