Home Labarai Rashawa Ta Ta’azzara Rashin Tsaro A Nijeriya – ICPC

Rashawa Ta Ta’azzara Rashin Tsaro A Nijeriya – ICPC

164
0

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce yawaitar cin hanci da rashawa ke rura wutar matsalar rashin tsaro a Nijeriya.

Farfesan ya bayyana haka ne, a wajen wani taron wuni biyu na kwamitin majalisar wakilai a kan yaki da cin hanci da rashawa da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokaradiyya ta Nijeriyar ta shirya a Abuja.

Owasanoye, ya zargi wasu ‘yan majalisar dokokin Nijeriya da manyan hafsoshin soji da hannu a matsalar cin hanci da rashawa, tare da bukatar su kaurace wa laifuffukan da ke haifar da matsalolin tsaro.

Ya ce Satar da manyan jami’ai ke yi ta lalata rundunar sojin Nijeriya, kuma ta raunana karfin gwiwar dakarun da ke fagen daga tare da tsawaita yakin da ake yi da ‘yan ta’adda.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana munguno, ya taba yin korafi a bainar jama’a cewa sun gaza yin bayani a kan kudaden da aka fitar domin sayen makamai a lokacin manyan hafsan hafsoshin sojin da su ka gabata.

Leave a Reply