Home Labarai Gwamnatin Kaduna Ta Nuna Damuwa Kan Cunkoso A Hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnatin Kaduna Ta Nuna Damuwa Kan Cunkoso A Hanyar Kaduna-Abuja

56
0

Gwamnatin jihar Kaduna, ta nuna damuwa a kan cunkoson da matafiya ke fuskanta a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wata Sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce yanzu haka su na kan tattaunawa da kamfanin Julius Berger da sauran masu ruwa da tsaki da ke aikin hanyar don ganin an warware matsalar.

Matafiya da ke bin ta Kaduna don zuwa Abuja da sauran biranen Nijeriya su na shan bakar wahala kafin su iya wuce matsanancin cunkoson da ke garin Kaduna.

An dai shafe tsawon lokaci gwamnatin tarayya ta na aikin gina titin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna da Kano, amma a lokuta da dama wasu na sukar tafiyar hawainiyar da aikin ke yi, da kuma yadda ake samun cunkoso da hatsari ga matafiya.