Home Home Rashawa: ICPC Ta Kwace Gidaje 97, Ta Rufe Asusun Banki 1,233 Na...

Rashawa: ICPC Ta Kwace Gidaje 97, Ta Rufe Asusun Banki 1,233 Na Wadanda Ake Zargi

28
0

Hukumar yaƙi da ayyukan cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC ta ce ta ƙwace gidaje aƙalla 97 daga hannun mutane daban-daban cikin shekara huɗu da suka wuce.

Hukumar ta ce cikin jerin kadarorin da ta ƙwace akwai gine-gine 33, da filaye, da wata ma’aikata waɗanda hukumar ta ƙwace daga wajen Dr Jimoh Olatunde, tsohon akanta a hukumar shirya jarrabawa ta JAMB.

ICPC ta bayyana wa Jaridar Punch cewa ta kuma garƙame asusun ajiya 1,233 tun daga 2019 zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Bugu da ƙari, 60 daga cikin asusan mutanen da ake zargi da aikata rashawa, an miƙa su ga gwamnatin tarayya.

Ta ce asusan na ɗauke da kuɗi naira miliyan 547.7 da kuma dalar Amurka miliyan 669,248.89 jimilla.