Home Labaru Ranar Murna: ‘Yan Kasuwa Sun Yi Bikin Bude Iyakokin Nijeriya

Ranar Murna: ‘Yan Kasuwa Sun Yi Bikin Bude Iyakokin Nijeriya

87
0

‘Yan kasuwa daga Jamhuriyar Benin da Nijeriya, sun gudanar
da bukukuwan murna sakamakon sake bude iyakokin da
gwamnatin tarayya ta yi.

Wata majiya ta ce, daruruwan mutane da su ka hada da ‘yan
kasuwa da masu motocin haya da na daukar kaya yanzu haka
sun mamaye iyakar su na jira a bude.

Wani jami’in kula da iyakar daga bangaren Benin, ya ce su na
bukatar samun umurni ne a hukumance domin a ba wa jama’a
damar fara tsallaka iyakar.

Wata ‘yar kasuwa da ake kira Jacquelline Watchinou, ta ce ta
zubda hawaye sakamakon sanar da bude iyakar, domin rufe
iyakar ya tilasta mata karbar aikin share gida domin ciyar da
iyalan ta.