Home Labaru Kasuwanci Rahoton NBS Ya Ce Farashin Kaya A Najeriya Ya Ragu A Watan...

Rahoton NBS Ya Ce Farashin Kaya A Najeriya Ya Ragu A Watan Satumba

11
0

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, wato National Bureau of Statistics NBS ta ce hauhawar farashin kaya a Najeriya ta ɗan ragu da kashi 0.38 cikin 100 a watan Satumba da ya gabata.

NBS tace an samu raguwar ce cikin rahoton da ta fitar, wanda ya nuna alƙaluman na watan Satumba a kan kasha 16.63 cikin 100 saɓanin kasha 17.01 da aka samu a Agusta.

Hukumar ta ƙara da cewa hauhawar farashin ya ragu a birane inda aka samu kashi 17.19 daga 17.59 da aka samu a Agusta, shi kuma na ƙauyuka aka samu 16.08 saɓanin 16.45.

Bugu da ƙari, hauhawar farashin kayan abinci ta ragu zuwa kashi 19.57 idan aka kwatanta da 20.30 da aka samu a watan Agusta.

Hukumar ta ɗora alhakin tashin farashin kayan abincin a kan tashin farashin da wasu kayan suka yi da suka haɗa da mai, da burodi, da kayan hatsi, da kifi, da gahawa (coffee), da dankalin Turawa, da doya, da madara, da ƙwai da dai sauran su.