Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Tsaida Ranar Talata 19 Watan Oktoba A Matsayin Ranar...

Gwamnatin Tarayya Ta Tsaida Ranar Talata 19 Watan Oktoba A Matsayin Ranar Hutu

15
0

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata 19 ga watan Oktoban 2021, a matsayin ranar hutu domin bikin maulidi da tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Shu’aib Belgore.

Sanarwar ta ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola yana taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyeyyen halitta.

Ya gargadi dukkan ’yan Najeriya da su zama masu hakuri da juriya tare da koyi da kyawawan dabi’u na Annabi, yana mai cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

Kazalika, ya yi kiran a kaucewa aikata abubuwan da za su kawo rarrabuwar kai a tsakanin al’ummar kasa sai ya bukaci dukkan ’yan Najeriya musamman matasa, su rungumi dabi’un aiki tukuru da kauracewa zaman kashe wando.

Ya jadadda cewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba za ta gushe ba wajen ci gaba da hada kan daukacin ‘yan kasa baki daya.