Home Labaru Rahoto: Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya 72 Sun Mutu A Bana – Guterres

Rahoto: Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya 72 Sun Mutu A Bana – Guterres

242
0
Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya 72 Sun Mutu A Bana - Guterres
Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya 72 Sun Mutu A Bana - Guterres

A wani rahoto da aka ruwaito, majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa ta yi asarar ma’aikatan ta 72 da su ka rasa rayukan su a wannan shekarar.

Karanta Wannan: Kididdiga: Al’ummar Duniya Za Su Zarce Fiye Da Biliyan Tara A Shekara Ta 2050 – MDD

Babban Sakataren majalisar Antonio Guterres ya tabbatar da hakan, a wajen wani babban taron sanya furanni domin tunawa da ranar ma’aikatan majalisar a birnin New York na kasar Amurka.

Ya ce daga cikin wadanda su ka mutu akwai fararen hula 25, yayin da 43 su ka kasance jami’an samar da zaman lafiya da kuma ‘yan sanda guda 4.

A cewar sa, ma’aikatan sun sadaukar da rayukan su wajen aiki a wurare masu hadari a duniya, wanda ya ce babu shakka sun cancanci yabo marar misali.

Guterres, ya kuma mika sakon ta’aziya ga iyalai da ‘yan uwa da mukusan ta da masoyan ma’aikatan majalisar da su ka mutu wajen kare martabar duk wani bil-Adama da ke doron kasa.