Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ba gaskiya ba ne labarin da ake yadawa kan cewa gwamnatinsa za ta kashe Naira biliyan 6 wajen rabon abincin buɗa baki a wannan wata na Azumin Ramadana.
Gwamnan ya yi watsi da jita-jitar ce cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa, naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari da casa’in da bakwai da dubu saba’in gwamnatinsa ta ware domin aikin ciyarwar sabanin yadda ake ikirari.
A bayan nan aka rika cece-kuce bayan bullar rahoton cewa gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan shida a matsayin kudin da za ta kashe wajen rabon abincin azumi.
Dangane da hakan ne Gwamnan Kano ya yi kira ga kafofin watsa labarai da su rika tabbatar da sahihancin bayanai gabanin watsa wa al’umma.